Nijar:Yunkurin kara tabbatar da zaman lafiya a Jihar Diffa | Siyasa | DW | 23.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Kungiyar Care Ita ce ta shirya wannan tattaunawa

Nijar:Yunkurin kara tabbatar da zaman lafiya a Jihar Diffa

Musulmi da Kirista a Jihar Diffa da ke a gabashin Jamhuriyar Nijar sun gudanar da wata tattaunawa domin kara samar da zaman lafiya a Jihar.

Wannan dai shi ne karo na farko ke'nan da aka gudanar da irin wannan taro tsakanin Muslmin da Kirista a karkashin jagorancin Kungiyar Care International.Jihar dai ta Diffa ta yi fama da rikicin Boko Haram shekaru da dama kafin daga bisani a ciwo kan lamarin.Kuma shugabannin addinin na ganin akwai bukatar a kara fadikar da jama'a a ame da mahimmancin zaman lafiya da kuma cundanya tsakanin al'umomin yankin.Musulimin da Kirista sun yi kira ga gwamnati da ta kara ba da kulawa wajen tabbatar da zaman lafiya wanda har ya zuwa yanzu a kan samun hare-hare na Kungiyar Boko Haram a Diffa jefi-jefi.

Sauti da bidiyo akan labarin