Nijar:Tsokacin jam'iyyun adawa
September 28, 2017Talla
Wannan ba shi ne karon farko ba da 'yan adawar na Jamhuriyar Nijar ke yin korafe-korafe na rashin halin ko in kula da gwamnatin ke nunawa a game da halin da al'ummar kasar ta samu kan ta a ciki na rashin ababen more rayuwa. Sannan kuma ga tsananin tsadar rayuwa da kuma talauci da ke adabar al'umma. Daya daga cikin shugabanin 'yan adawar na Njar dan majalisa Soumana Sanda ya ce abin takaici halin da al'ummar Nijar take a ciki a yanzu.