Nijar:Jam'iyyar MNRD ta raba gari da MNSD
March 28, 2017Talla
Jam'iyyar ta MNRD Hankuri da tsohon shugaban kasar Alhaji Mahamane Ousmane wanda ya yi takara da ita a zabubukan da suka gabata na watan a shekara ta 2016 na a matsayin babbar jam'iyyar da ke dasawa da jam'iyyar Mnsd nassara wacce shugabanninta ta hanyar wani dadden kawance suka mulki Jamhuriyar Nijar har na tsawon shekaru da dama.Amma a yanzu sun raba gari saboda MNSD Nasara ta bi bayan gwamnatin.
Wannan lamari dai da ya faru na ficewar 'yan majalisun na MNRD daga kawance da suke yi da MNSD a majalisar zai iya kara wa 'yan adawar karfi musammun ma jam'iyyar Modem Lumana ta Hama Amadou.Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da ake samun canje-canje na jam'iyyun siyasa a Nijar ba.