Nijar: Zargin ′yan adawa da zagon kasa | Siyasa | DW | 22.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Zargin 'yan adawa da zagon kasa

Jam’iyyar PNDS Tarayya na zargin abokiyar hamayya ta Lumana Afirka da kasancewa kanwa uwar gami wajen dagula al’amuran da ke addabar kasar ta hanyar gamin baki da sauran bangarori da ke fatan haddasa fitina.

Kawancen jam'iyyun na MRN a gabansu jam'iyyar PNDS Tarayya da suka jagoranci taron na zargin bangaren jam'iyyar hamayya musamman ta Lumana Afirka wato Jam'iyyar tsohon Firaminista Hama Amadou da zama tushen duk wata tashin tashina da ke addabar kasar, dauko daga takkadamar da taki karewa da ja-in-ja mai zafin gaske tsakanin gwamnati da malaman makarantun boko, har izuwa ga batun shari'ar gwamnati da Africard inda Nijer ke kan hanyar hasarar makudan kudade acewar su, da ma bullo da batun badakalar wawurar kudi sama da miliyan dubu 200 da a ke zargin wani kusa a cikin jam'iyyar da ke mulki Hassoumi Masaoudou da aikatawa. Duk wadannan ba komai ba ne face wasu sabbin sale-sali da makarkashiya don kifar da gwamnatin  hadaka.

Malam Kalla Moutary mamba ne a kwamitin zartarwa na jam'iyyar PNDS, kusa kuma a kawancen jam'iyyun da ke mulki, ya ce "Yau 'yan darikar LUMANA su ke cewa mu ne masu yin harkokin ashsha ba'a jin alheri a bakinsu sai dai sharri."

Ko baya ga batutuwan tattalin arziki da almundahana da dukiyar kasa wani babban batun da kawancen na mulki ya mayarwa 'yan adawa da martani akai shi ne na fannin tsaro da ke addabar kasar inda ya ce ansamu nasara.


Sai dai da ta ke mayar da martani babbar jam'iyyar Hamayya ta Lumana Afirka ta bakin mukaddashin shugabanta Oumarou Noma ta ce su kam sam ko in kula bisa zargin zama kanwa uwar gami da PNDS ke yi wa jam'iyyar hasali ma kalamun na kawancen masu mulkin tamkar haushin dan kwikuyo ne da baya tada hankalin dan giwa.

Sauti da bidiyo akan labarin