Nijar: ′Yan kwadago na so a yi yajin aiki | Labarai | DW | 28.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: 'Yan kwadago na so a yi yajin aiki

Kungiyoyin fararen hula da na kwadago sun bukaci jama'a da su shiga yajin aiki saboda yin karen tsaye da hukumomi ke yi wa tsarin dimokradiyya.

Shugabannin kungiyoyin fararen hula na da 'yan kwadago a Nijar sun nemi masu sana'a da su kauracewa wuraren sana'o'insu don nuna rashin jin dadinsu game da rashin aiwatar da dimokadiyya kamar yadda ya dace a kasar wanda gwamnatin Shugaba Issoufou Mouhammadou ke yi.

Wakilinmu na Yamai Mahamman Kanta ya ce kungiyoyin sun ambata hakan ne dazu a wani taron manema labarai da suka kira. To sai dai duk da wannan kira da 'yan kwadagon suka yi, 'yan kasuwa a babbar kasuwar da ke birnin Yamai na cigaba da kasuwancinsu.