1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Tsawaita majalisun kananan hukumomi

Abdoulaye Mamane Amadou | Salissou Boukari
February 19, 2018

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauki matakin tsawaitawa tare da rusa wasu majalisun kananan hukumomi na kasar da kuma tsige wani shugaban karamar hukuma bisa zargin almundahana da dukiyar kasa.

https://p.dw.com/p/2svYd
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Shugaban kasar Nijar Issoufou MahamadouHoto: DW/M. Kanta

A yayin wani zaman taron majalisar ministocin ne da ya gudana a karshen makon da ya gabata ne dai gwamnatin ta Nijar ta bayyana matakin tsawaita wa'adin majalisun kananan hukumomi fiye da 200 bisa amfani da wata ayar doka mai lamba 180 da ke cikin kundin tsarin tafiyar da kananan hukumomi "code de collectivites teritorieles" da aka yi wa gyaran fuska a cikin watan Oktoba na 2016 da zummar baiwa gwamnati karfin iko na kara tsawaita wa'adin kananan hukumomin kasar 265 bisa hujjar samun wadataccen lokacin shirya zabukan kananan hukumomin.

Niger Niamey Proteste AREVA Uran
Majalisar dokokin NijarHoto: DWM. Kanta

Matakin da ke a matsayin irinsa na shida, ya baiwa wasu kanan hukumomin kasar sabon wa'adi na watanni shida gami da Kantomomin yankin Da'irar birnin Yamai da gwamnatin ta na da a matsayi na wucin gadi. Sai dai tun ba'a je ko ina ba matakin na ci gaba da hadasa tayar da jijiyoyin wuya. Sai dai ko baya ga batun tsawaita wa'adin kananan hukumomin, gwamnatin ta kuma dauki matakin rusa wasu majalisun kananan hukumomi uku da suka hada da Golle a yankin jihar Dosso Tesker a yankin jihar Damagaram da kuma majalisar mashawartan karkara ta Dakoro da ke yankin jihar Maradi, bisa zarginsu da aikata laifukan rashin iya jagoranci bayan an tura masu jami'an bincike daga Birnin Yamai.

Nouhou Arzika
Dan fafutikar kare demokradiyya Nouhou ArzikaHoto: DW/T.Mösch

Taron majalisar ministocin na Nijar ya kuma Tsige Malam Maman Issaka daga mukaminsa na shugaban gundumar Garagumsa da ke jihar Damagaram ta hanyar amfani da ayar doka mai lamba 63, inda aka zargeshi da karkara dukiyar kasa gami da sayar da filaye ba tare da ka'ida ba, sannan da rashin iya jagoranci. Tun dai da jimawa, kungiyoyin rajin kare demokaradiyya ke matsin lamba ga gwamanti kan cewa a shirya zaben kananan hukumomi don kaucewa matsalolin rashin iya jagorancin da ake fuskanta a akasarin kananan hukumomin. Sai dai shekaru uku zuwa yanzu gwamnatin ta Nijar ta ce bata da halin shirya zaben, abun da  wasu ke yi wa kallon tamkar wata yar manuniya ce ga zabubka masu zuwa na 2021 a kasar.