1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Tsabtace kundin rajistan masu zabe

Salissou BoukariDecember 29, 2015

A wannan Talatar ce wakillan hukumar OIF ta kasashe masu magana da harshen faransanci ke fara wani aikin tantance kundin rajistan masu zabe a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/1HVb7
Ibrahim Boubé
Me Ibrahim Boubé Shugaban hukumar zaben NijarHoto: DW/M. Kanta

A kalla dai kwararru guda hudu ne hukumar ta OIF ta turo a karkashin jagorancin Janar Siaka Sangare dan kasar Mali, inda tun a jiya Litinin suka yi zama na farko da wakilan hukumar zaben kasar kafin daga bisani su tsunduma cikin aikin binciken a wannan Talatar a cewar Kadri Oumarou Sanda mataimakin shugaban hukumar zaben kasar ta Nijar.

Wannan hukumar dai ta taka rawar gani wajan binciken jerin sunayan masu zabe a kasashe kamar su Togo, Benin da kuma ta baya-bayannan kasar Burkina Faso wanda suka gudanar da zabukansu ba tare da matsaloli ba. Hukumar zaben kasar ta Nijar ce dai CENI ta yi kira ga hukumar da OIF da ta duba kundin rajistan na Nijar kamar yadda 'yan adawar kasar da sauran kungiyoyin fararan hulla suka bukaci hakan kafin a fuskanci zabukan kasar na watan Febireru.