Nijar: Taron jam′iyyu don sasanta rikicin Siyasa | Siyasa | DW | 29.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Taron jam'iyyu don sasanta rikicin Siyasa

Hukumar kula da dimukaradiyya ta Amirka NDI da kungiyoyin duniya da ke da rajin kare kyakyawan mulki ne suka shirwa taron a Nijar, wanda ya hada 'yan siyasa da wakilan kungiyoyin da ke da rajin wanzar da zaman lafiya.

 

Watanni shida baya kafin a zo taron na wanna Talatar hukumar NDI ta aika wata tawagar da ta hada wakilan kungiyoyin da ke kawo mata goyon baya ta yi rangadin cikin jihohi, birni da karkarar Nijar, Inda ta gana da al'ummar jamaa, da ganin irin tarin matsalolin da suke fama da su, wadanda suka hada da tabarbarewar ilimi, karancin kiwon lafiyar jiki a gidajen asibitoci, talauci da uwa uba matsalar tabarbarewar tsaro.

A cewar Mousa Changari shugaban hadaddiyar kungiyar da ke rajin kare hakin bani adama da ake kira Alternative Espace Citoyenne, kula da rashin ilimi da kiwon lafiya da tsaro na gaban komai.

Shi ma Alhaji Moutapha Kadi shugaban hukumar sulhunta 'yan kasa wato Mediateur National, cewa ya yi taskar kasuwance ma ta gurbace, jami'an Douane ko Costum sun kara kudin awon kaya, wanda ya sa kaya sun yi tsada rayuwa ta yi tsada zasu kai kuka wajen gwamnati.

Bangaren siyasa da yake nan ne babbar matsalar majalisar sasanta rikicin siyasa wato CNDP wada bangaren adawa sun kauracewa halartan taron domin 'yan adawan sun ce su zaben da aka yi na watan Afirilun da ya gabata ba su yarda da shi ba. A cewarsu hukumomin da wannan zaben ya dora haramtattu ne a garesu a cewar kakakin gungun jam'iyun kawance adawa.

A nasu wajen  Ibrahim Bage wakilin jam'iyun kawance da ke mulki 'yan adawa basu da gaskiya a kan wannan batun amma abin da ya kamata su yi a zauna teburin taunawa, kowa ya fadi ra'ayinsa,shi ne siyasa amma ba gaba ba.

 

Sauti da bidiyo akan labarin