1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta wayi gari cikin tashin hankali

May 23, 2013

Gwamnatin Nija ta tabbatar da cewa kimanin sojojinta 20 ne su ka kwanta dama yayin da wasunsu su kimanin 70 su ka ji rauni a sakamakon wasu tagwayan har- hare a birnin Agadez.

https://p.dw.com/p/18ctm
epa03142091 President of Niger, Mahamadou Issoufou delivers a speech during the opening ceremony of the 6th World water forum at Parc Chanot in Marseille, southern France, 12 March 2012. More than 1,000 high-level stakeholders are gathered in Marseille to share solutions to worldwide water problems and commit themselves to their implementation. EPA/GUILLAUME HORCAJUELO +++(c) dpa - Bildfunk+++
Niger Mahamadou IssoufouHoto: picture-alliance/dpa

Wasu mutane da gwamnatin kasar ta ce tana kyauttata zaton mambobin kungiyoyin masu tsanannin kishin islama ne su ka kai hari a barikin sojin garin Agadas da kuma cibiyar kamfanin hakar uranium na Somair da ke a garin Arlit.

Zaman rudani da fargaba

Tuni kuma alummomin yankin arewacin kasar su ka shiga cikin halin zaman dar-dar. Bayanan daga hukuma sun nunar da cewa da misalin karfe 5 da kwata na asubahin a lokacin da jama'a ke haramar zuwa sallar asuba ne maharan su ka kai harin nasu a lokaci daya a garin na Agadas da kuma na Arlit da ke a yankin arewacin kasar . A garin Agadas wasu mutane ne su biyar fararen fata a cikin motoci biyu kirar Toyota su ka afka wa barikinn sojan ta Zone de Deffence Numero 2 ta garin na Agadas a yayin da a garin Arlit wata mota ce ita ma kirar Toyota dauke da mutane biyu fararen fata su ka kai harin kunar bakin wake akan wasu manyan na'urorin aiki na kamfanin uranium na Somair. Tuni kuma hukumomin tsaro na kasar su ka gudanar da taron gaggawa inda su ka yi bitar lamarin da ya afku. Kuma bayan kammala taron ministan cikin gida Malam Abdou Labo ya bayyana wa manema labrai sakamakon barnar da wadannan har- hare biyu su ka yi a garuruwan guda biyu.

Niger Agadez Freitagsgebet
Hoto: picture-alliance/ dpa

Tuni dai wadannan hare-hare su ka saka alummomin mazauna wadannan garuruwa cikin halin zaman dar-dar kamar dai yanda wani malami mazaunin garin na Arlit da aka tuntuba ta wayar salula ya shaida.

Tsaiko ga akin kanfanin Somair

Hukumomin Nijar sun ce ya zuwa yanzu ba su da tabbaci akan wadanda su ka kai wadannan hare-hare amma suna kyautata zaton cewa kungiyoyin 'yan ta'adda ne masu tsanananin kishin Islama wadanda aka kora daga Mali da dama ba tun yau ba su ke da labarin suna son kawo har- hare a cikin kasar.

Niger Uranmine Areva Somair in Arlit Archivbild
Hoto: picture alliance/AP Photo

Yanzu haka dai gwamnati ta ce barnar da ta afku harin da aka kai a kamfanin Somair zato janyo dakatar da aikin kamfaninn na wani dan lokaci. Kuma tuni su ka killace yankunan da lamarin ya shafa da sojoji sannan kuma sun kaddamar da zaman makoki na kwanaki ukku a duk fadin kasar sabili da afkuwar wanann lamari na assha.

Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Halima Balaraba Abbas