1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta kafa dokar ta-baci a jihar Diffa

Gazali Abdou TasawaOctober 15, 2015

Gwamnatin kasar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin karfafa matakan tsaro a yanki wanda Kungiyar Boko Haram ta zafafa kai hare-harenta a cikinsa a baya bayan nan.

https://p.dw.com/p/1Gock
Soldaten im Niger
Hoto: Desmazes/AFP/Getty Images

Dokar ta baci ta wa'adin kwanaki 15 a yankin Jihar Diffa na Kudu maso Gabashin kasar mai fama da hare-haren Kungiyar Boko Haram. Kamfanin dillanci labaran Reuters ya ruwaito cewa gwamnatin kasar ta bayana daukar wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da aka gabatar a gidan talabijin na kasa a jiya Laraba.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne domin samun damar karfafa matakkan tsaro da na hana yawan dare dama takaita zirga-zirgar jama'a a dukiyoyinsu a wannan yanki da ke kan iyaka da makobciyar kasar Najeriya inda mutane akalla 40 suka halaka a makonnin baya bayan nan a sakamakon hare-haren Kungiyar Boko Haram.

Mutane kimanin dubu da dari daya ne hukumomin kasar ta Nijar suke tsare da su a bisa zarginsu da kasancewa 'ya'yan Kungiyar ta Boko haram wacce wasu alkalumma da hukumomin kasar ta Nijar suka wallafa a ranar Juma'ar da ta gabata suka nunar da cewa ta kaddamar da hare-hare akala 57 a cikin jihar ta Diffa daga watan Febraru zuwa yanzu.