1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moodys: Nijar ta gaza biyan basussukan da ta ranto

Gazali Abdou Tasawa AH
January 24, 2024

Cibiyar bincike da nazari kar harkokin basussukan kasa da kasa ta Mooodys ta bayyana cewa Nijar na ci gaba da kasa biyan basussukan da ake biyar ta sakamakon takunkuman kariyar tattalin arzikin.

https://p.dw.com/p/4bd3J
Hoto: REUTERS

 Nijar ta fada cikin wannanmatsala ce saboda takunkuman da kungiyoyin ECOWAS da UEMOA suka saka wa kasar a dalilin juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata. Cibiyar binciken ta ce matsalar basussukan kasar ta Nijar na neman haddasa matsalolin kudi ga bankunan kasashen Afirka ta Yamma da dama. 

Basussuka da Nijar ta gaza biya a tsawon watanni shida

Niger Sitz der französischen Firma Somair in Niamey
Hoto: Joerg Boethling/IMAGO

Rahoton cibiyar ta Moody,s ya bayyana cewa ko a wannan wata Nijar ta kasa biyan bashin kudi miliyan 38 da dubu 700. Kuma a tsawo watanni shida bayan juyin mulki a jumulce bashin kudin da Nijar din ba ta biya ba ya kai na  Dalar Amirka miliyan 485. Lamarin da cibiyar ta ce ya soma haddasa matsalar karancin kudi shiga a bankunan yankin da dama wanda kuma ke zama wata barazana ga jarinsu da ma makomarsu. To amma wasu masu adawa da gwamnatin mulkin sojan Nijar na ganin ba wanda ya kamata a yi kuka da shi kan wannan matsala ta Nijar illa hukumomin mulkin sojan da suka yi juyin mulki a kasar. 

Fargaban 'yan Nijar a kan wannan al'amari 

Banknoten CFA Francs
Hoto: SEYLLOU/AFP

wasu ‘yan Nija din dai na ganin hanya daya ta shawo kan wannan matsala ta kudi da ma sauran matsalolin Nijar ita ce hawa tebirin sulhu da kungiyar ECOWAS. Cibiyar ta Moody, s ta ce idan har aka wuce watanni shida to kuwa za a saka Nijar a jerin kasashe maras tabbas ga harkokin bashi, wadanda ba su  bashi ke zama hadari.