Nijar: Shekara daya bayan yamutsin dalibai
April 10, 2018Talla
Kusan dukkan dalibai sun dakatar da karatu a cikin dukkanin makarantu gwamnati da ma masu zaman kansu domin nuna alhini a zagayowar cikar shekara guda da kisan da 'yan sanda suka yi wa Mala Bagalé Kelloumi. A halin da ake ciki daliban na kokawa game da yadda har kawo yanzu gwamnatin ta Nijar ta gaza hukunta wadanda ke da hannu a kisan na daliban, duk kuwa da cewar gwamnatin ta girka wani kwamitin da ke gudanar da bincike.
Tun daga shekara bara daliban sun shiga cikin wani hali na yau karatu gobe yajin aiki sakamakon yadda suka ce gwamnatin ta yi yarjejeniya da su a kan bukatunsu amma kuma ta gaza cika alkawari.