Nijar: Makaho mai tukin amalanke da sana'ar salula
November 23, 2016A yankin Damagaram na Jamhuriyar Niger wani matashin makafo ne mai sunan Ibrahim Mansur dan shekaru 25 da haihuwa Allah ya hore ma baiwa ta iya tukin amalanke da kuma sana'ar aikawa da kudi a wayar salula da ake kira shap-shap a kasar ta Nijar, sana’ar da a wani lokaci ma take gagarar masu idanu.
Shi dai Ibrahim Mansur matashin makaho ne dan asalin garin Geza Mahaman da ke a cikin karamar gundumar Mirriah da ke a yankin Damagaram. Ya samu nakasar makafta ne a sakamakon kamuwa da cutar dussa ko tininim tun yana dan shekaru biyar a duniya. Amma duk da haka a yanzu Allah ya yi masa baiwa ta iya gudanar da ayyuka daban-daban da suka hada da sana'ar aika kudi a salula gami da yin dashen layi.
A kuma matsayinsa na mazaunin karkara yana gudanar da aikace aikacen gida ta hanyar jan amalanken shanu da kai taki gona don samun dan na sakawa a bakin salati da nufin kauracewa shiga bara kamar yadda ga al'ada makafi ke yi a kasashen Afirka da dama. Jama'a da dama ne a garin na Damagaram ke mu'amala da makahon a cikin aikin nasa dama nuna mamakinsu dangane da baiwar da Allah ya huwace masa. Sun kuma bayyana gamsuwarsu dangane da yadda ya kama wannan hanya a maimakon yin bara.