Nijar: Issoufou ba zai yi tazarce ba
April 3, 2017Shugaba Mahamadou Issoufou wanda ya bayyana hakan ga manema labarai, ya kara da cewa yana fatan kasancewa shugaba na farko a tarihin kasar da zai damka mulki a hannun wani shugaban da 'yan Nijar za su zaba a shekara ta 2021 mai zuwa. Ya kara da cewa: "Ni dan siyasa ne tsantsa kuma ba ni da girman kan cewar ba wani sai ni kadai ke iya jagorancin kasa, da akwai yan Nijer da dama da ke iya rike wannan matsayi, saboda haka fatana shi ne in shirya zabe mai tsabta tare da mika mika mulki ga hannun wani da al'ummar Nijar suka zaba, kuma ina jan hankulanku da cewar wannan zai zama karon farko a tarihin Nijar tun samun 'yancin kai."
Ko kalamansa sun karyata zargi?
Ba tun yau ba dai bangarori daban-daban na kasar ke ta hasashen take taken shugaban na makalewa a kan madafun iko duba da yanayi da halin tafiyar demokradiya a kasar mai cike da sarkakiya, sai dai wadanan kalamai na shugaban kasa tun daga yanzu sun haifar da da ra'ayoyi daban-daban kama daga fannin 'yan siyasa zuwa ga masu sharhi a fagen na Demokradiyya. Malam Sama'ila Amadou dan siyasa ne kuma shugaban jam'iyyar Awaiwaya na da ra'ayin cewa Shugaba Issoufou ya zuba ruwa ga wannan wuta. Wasu kungiyoyin fararen hula da ke rajin kare hakkin dimokradiyya kuwa na ganin in ba rami mai ya kawo batun ramin, ma'ana in dai ba yana da burin yin tazarcen ba mai ya kawo zancen tun yana da shekara guda a kan mulki? Sai dai ga wani mai sharhi a kan al'amurran yau da kullum kuma dan fafatukar kare hakkin dan Adam Alhaji Salissou Amadou na da ra'ayin cewa lokaci bai yi ba a yanzu, da ya kamata a soma wannan cece-kuce, yana mai cewa abin da ya kamata a sa a gaba a yanzu shi ne batun warware dinbin matsalolin da kasar ke ciki.