1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Shiga

Nijar: Horas da matasa ilimin zamani

A jihar Tawa da ke Jamhuriyar Niger wani matashi ya bude wani gidan horas da matasa fusahohin kimiya da na ilimi na zamani a wani mataki na fidda musu kwadayin zuwa kasashen Turai domin neman ilimi.

 

Jihar Tawa na zama sahun gaba a cikin yankunan kasar Niger inda matasa ke yawan kwarara kasashen wage ciki ko har da na Turai imma wurin ci rani ne ko kuma wurin karin ilimi musamman a wannan lokacin da ilimi mai zurfi ke zama kofar shiga zamani. Kuma ganin yadda wannan bukatar ke dada karuwa a wannan rukunin al'umma ne a Jihar, wani matashi dan kimamin shekaru 35 da haihuwa, Elhaj Abdoul Azize Ramba ya bude wani katafarin gidan horas da matasan fusas'o'in kimiya da na ilimi mai zurfi harma da na tattali domin basu damar tsayawa gida ba sai sun fita ba kamar yadda ya shaida wa DW: 

"Dalilin da ya sa shi ne, nan jihar Tawa mutane suna yawan tahiya wajen bida to saboda haka gaskiya suna cikin abubuwan da suka ja hankalinmu muka ga bari mu zo nan mu kafa wannan shiri, da fatan zai ja hankalinsu su rage yawan tafiya bidar ilimi wani guri tunda abin da suke nema ya samu a gida". 

Wannan dai ba karamin ci-gaba ne ba ga matasan da suka fara ganowa wadanda kuma suka fara samu aiki walau na dindindin ko kuma na wucin gadi bayan kammala samun horon a gurin Abdoulaziz kamar yadda ya kara bayani: 

 
"Na so a ce na samu kiyasi muna nan ga bincike amma ba mu da cikakken kiyasi na mutun nawa suka samu aiki a halin yanzu na dindindin, mutun nawa suka samu aiki na gajeran lokaci duk cikin wadanda mu ka horas suna samun aiki"
 
Daidai da yadda jami'a ke yi shima Abdoulaziz Ramba na rike daliban ne tsawon wani lokaci kafin ya kai ga yaye. Amadou Hassan na daga cikin daliban da aka yaye a wannan makaranta ta horas da matasan:

 
"Mu nan ana koya mana ba sai ka nemi aiki wani guri ba, kai da kanka kana iya kirkira wani aiki har wani ma ya samu, ba sai mun jira aikin gwamnati ba, mu da kanmu muna iya mu kirkiro kanfani na kanmu don mu yi aiki mu tsaya ilimin da muka samu ya muna amfani nan cikin kasarmu shi ne babban burinmu".


 

Babu shakka matasa a yanzu sun fi gwammace wa aiki a ofis a maimakon aikin hannu. Laila Ousman Adamou ta share shekaru uku tana karbar horo a wurin Abdoulaziz, ta kuma bukaci tsayawa gida ne sabanin tunaninta a can farko inda ta so tafiya wage karatun:
 
 
"Tabbas mutane suna ganin kamar idan suka fita zuwa kamar Ingila ko dai wata kasa ta Turai duk suna samun albashi wanda ya fi wanda za'a basu cikin kasarsu. An fada a ce dan wane ya tafi wanga gari karatu, amma ni gaskiya na kwammace in tsaya nan. Cikin kasarmu aka bani ilimin nan in tsaya in yi wa kasa aiki da shi, al'ummar kasarmu su amfana"
 
Yanzu haka dai hukumomin da iyayen yara na alfahari da wannan dubarar da Abdoulaziz ya bullo da ita ta ragewa matasan tunanin fita waje.