Nijar: Dalibai sun yi zanga-zanga
July 22, 2017Talla
Jami'an tsaron 'yan sanda a jamhuriyar Nijar, sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tawartsa wata zanga-zangar dalibban jami'ar birnin Tahoua a a yau Asabar, inda kimanin dalibbai 11 suka samu raunuka yayin da aka tsare akalla guda takwas a ofishin 'yan sanda.
Duk da cewar dai ya zuwa yanzu kura ta kafa, hukumomin jihar sun jibge jami'an tsaron a mahimman wurare na birnin na Tahoua da ake kallo a matsayin magama ta dalibban. Wannan zaga-zangar da ke zuwa a lokacin hutun karatun, ta wakana ne bayan da dalibban jami'ar suka bukaci samun alawus-alawus.