Nijar: Bukatar tsabtace hukumar yaki da cin hanci | Siyasa | DW | 05.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Bukatar tsabtace hukumar yaki da cin hanci

Kungiyoyin masu zaman kansu a Nijar sun yi kira ga shugaba Mahamadou Issoufou da ya zage dantse wajen yakar matsalolin talauci da rashawa, da suka samu gindin zama.


Wanan korafi ko yunkurin kungiyoyin farar hula game da canja salon yaki da cin hanci da karbar rashawar dai, ya zo ne a kasa da mako guda da shan ratsuwar da shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya yi ta kama aiki.

Ko da yake a can baya ma dai al'ummar kasar sun sha korafi game da tafiyar hawainiya da aikin hukumar yakar cin hanci ke yi wanda a cewar Yahaya Badamassi daga Kungiyar RED ta kasa a shekarun da hukumar ta kwashe tana aiki bata tabuka komai ba.

Babban abin da masana ke hange shi ne makomar ci gaban kasar ta fanin tatalin arziki daga bangarori daban-daban na rayuwa. Abin jira a gani dai shi ne yadda wannan kira ta kungiyoyin farar hula za ta yi tasiri ga mahunkuntan na Nijar.

Sauti da bidiyo akan labarin