Nijar: Bincike kan karkatar da kudaden kasa | Siyasa | DW | 23.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Bincike kan karkatar da kudaden kasa

Hukumomi a Nijar na ci gaba da kama mutanen da ake zargi da aikata ba dai-dai ba ta hanyar karkata kudaden kasa a ma’aikatun gwamnati.

Akalla mutane 30 ne ko fiye da hakan hukumar ta 'yan sanda ta farin kaya ta gayyata don bada ba'asi kan zargin da ake musu na wawashe dukiyar kasa. An dai bankado wannan lamari ne bayan da gwamnatin ta gudanar da wani gagarumin bincike a ma’aikatu da dama, inda binciken ya yi nuni da cewar mutanen sun janyo wa gwamnati mummunar asara. Wadannan mutane dai sun hada da 'yan kasuwa da 'yan majalisa da kuma wasu tsofaffin ministoci. 

Rahotanni daga fannin shari’ar kasar dai na cewar daukacin wadanda ake rike dasu, galibinsu sun amince da aikata ba dai-dai ba yayin da tuni ma wasu suka fara biyan kudaden da suka wawashe. Tuni kungiyoyin 'yan fafatuka da masu yaki da cin hanci da rashawa suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan sabon lamari. Malam Kane Ila Jigo da ke zaman mamba a wasu kungiyoyin da ke yaki da cin hanci da rashawa ya ce: ''Duk wani wanda ya yi sama da fadi da dukiyar kasa to ya mayar.''

Wannan lamari dai na zuwa ne a ya yin da gwamnati ta ke cikin yanayi na matsa kaimi domin inganta rayuwar jam’a ta hanyar kakkabe duk wasu bata gari masu karkata dukiyar kasa, ta hanyar karfafa wa fannin shari’a musamman ma fannin da ke kula da bincike da shari’ar da ta shafi tattalin arziki. Sai dai kungiyoyin sun nemi da a kiyaye tare da tabbatar da adalci a cikin lamarin kamar yadda Malam Mamane na kungiyar ANLC mai wakiltar transparncy Nijar ya shaidawa DW a wata hira inda ya ce: ''Shari'a aba ce mai wuya domin siyasa na iya shiga, domin haka a yi aiki bisa ka'ida da nufin samun sukunin yin adalci''.

Yanzu haka dai hankali ya karkata kan abubuwan da za su biyo bayan wannan guguwar ta kame-kamen jama’a, wadanda a ke tuhuma da hannu a cikin salwantar da dukiyar kasa. A baya dai gwamnati ta sha yin yunkuri na hukunta masu ire-iren wadannan laifuka, sai dai sau tari yunkurin baya yin wani tasiri.

Sauti da bidiyo akan labarin