1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Barazanar da 'yan jarida ke fuskanta a yayin aiki

Abdoulaye Mamane Amadou
May 3, 2018

A Nijar kamar sauran kasashen duniya ana cigaba da gabatar da ranar tunawa da yan jarida ta duniya inda hukumomin kasar suka shirya tarukan tattaunawa da mahawara kan duba aikin jarida

https://p.dw.com/p/2x8Ch
Sudan Pressefreiheit Symbolbild
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Sai dai wani batun da ke cigaba da mamaye ranar shi ne muzgunawar da ake cigaba da yi wa wasu ciki har da Baba Alpha daya daga cikin 'yan jaridar kasar da aka zarga da aikata laifi da kuma tusa keyarsa zuwa kasar Mali.

Muhimman batutuwan da suka fi daukar hankali a ya yin bukukuwan na wannan shekara sun hada da duba halin da ake ciki na yancin fadar albarkacin baki a duniya musamman ma samun dama ta cikakkun labarai wajen aikin jarida.

 

Sai dai a Nijar a daura da duk wadannan da ma wasu mahimman tarukan da kugiyoyin 'yan jarida suke gudanarwa batun shari'a ga kafafen yada labarai ga yan jarida na daga cikin abubuwan da ke kan gaba wajen mamaye wannan rana.

Malam Lamine Soulaimane sakataren kungiyar masu kanfanonin yada labarai masu zaman kansu ne ya ce ta wannan fannin 'yan jarida na fuskantar babbar barazana.

Yeung Kin Yeung HKJA
Nemarwa 'yan jarida 'yanciHoto: HKJA

 

Ya ce "Kasan akwai yan jarida da suka kai kansu suka cewa Gwamnati gamu ku yi yanda kuka ga dama da mu to wadannan matsalolin da yan jarida ke fuskanta bata shafesu ba".

Ai ko biciken da kaga a na yi wa wasu 'yan jaridu kan batun haraji bata shafe su sai wasu wadanda ake da niyar a sha musu kai saboda tonon asirin da suke suna fadin halin da kasa ta ke ciki tonon asirin da suke yi don talakawa su sani shi ne ya sha masu kai suna son samun wata hanyar da zata kai su ga dakatar da hakan, tunda talakawa su na sanin abin da ake ciki to mu kuma mun ce wallahi ba su isa ba.

Afghanistan Trauer im getötete Menschen, darunter auch viele Journalisten
Karramawa 'yan jarida da suka rasa ransuHoto: picture-alliance/dpa/T. Mondal

 

A farkon watan Aprilun wannan shekarar ne dai hukumomin na Nijar suka kargame wani dan jarida mai zaman kansa Baba Alpha da mahaifinsa Alpha Mohamed sakamakon zarginsu da aikata laifi na mallakar takardun da ba na gaskiya ba.

 

Lamarin da kuma ya kai hukumomin tusa keyar Baba Alpha din har izuwa kan iyakar kasar da Mali jim kadan bayan wata kotu ta sallameshi bisa zargin kasancewa wata babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasar.