1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An zargi Shugaba Issoufou da cin amanar kasa

Mahaman Kanta/ASSeptember 8, 2015

Shugabannin kawancen jam'iyun adawan Niger sun nemi majalisar dokokin kasar da ta gaggauta tuhumar shugaba Mahamadou Issoufou kan zargin cin amanar kasa.

https://p.dw.com/p/1GTKU
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

'Yan majalisar dai sun bijiro da wannan batu ne da nufin ganin shugaban na Nijar Mouhamadou Issoufu ya amsa tuhuma kan cin amanar kasa bayan da suka ce a lokuta da dama ya taka dokar kasa ciki kuwa har da umarnin da suka gwamnatinsa ta bada na sakin wasu makudan kudaden da aka kama a filin jirgin saman Yamai ba tare da hukunta wanda za su fita da kudin daga kasar ba kamar yadda doka ta tanada.

Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Da ya ke tsokaci kan wannan batu bayan bayan wani taron manema labarai da 'yan adawar suka gudanar a birnin na Yamai, shugaban jam'iyyar ORDN Tauraruwa da ke cikin kawancen kungiyar 'yan adawar Dakta Mamman Sani Adamou cewa ya yi ya kyautuwa a ce alkalin akalan kasar ya yi amfani da karfin ikon da doka ta bashi wajen yin bincike da kuma daukar mataki kan wanda ke da hannu a wannan batu.

Rashin daukar wannan mataki da 'yan adawar suka ce alkalin alkalan bai yi ba ne ya sanya suka yanke shawarar neman 'yan majalisar dokokin kasar da su gaggauta ajiye takarda ta tuhumarsa domin a cewarsu bai kamata a ce wanda aka zaba don kare dokokin kasa ya kuma kasance ya na taka su ba musamman da ya ke lokacin da ya yi rantsuwar kama aiki ya sha alwashi bin dokokin sau da kafa.

To sai dai jam'iyyar PNDS Tarayya ta Shugaba Issoufou din ta musan aikata laifi na cin kasa da ake zarginsa da shi kana ta nesanta shi da yin duk wani abinda ya saba dokokin kasar. Ibro Sani da ke zaman guda daga cikin kusoshin jam'iyyar ta PNDS Tarayya ya ce ko kusa 'yan adawar basu da wata hujja mai karfi kan wannan zargi da suke yi.

Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Wannan zazzafar takaddama ta kunno kai ne daidai lokacin da fagen siyasar Jamhuriyar Nijar din ke cigaba da daukar dumi musamman ma da ya ke ya an kama hanyar yin zaben gama-gari a kasar wanda zai gudana cikin watan Fabrairun shekara da ke kamawa, zaben da kungiyoyi na ciki da wajen kasar ke ta fafutukar ganin an yi shi lami lafiya.