1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An kaddamar da atisayen sojojin duniya

Abdoulaye Mamane Amadou RGB
April 11, 2018

An kaddamar da babban atisayen sojojin Amirka da na sauran kasashen duniya a Jamhuriyar Nijar don yakar safarar makamai da kuma ayyukan ta’addanci da ke kara kamari a yankin.

https://p.dw.com/p/2vsb3
Symbolbild Senegal Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Akalla sojojin kasashen Afrika 12 da wasu 14 na kasashen duniya ciki har da Jamus da Faransa ke halartar babban atisayen da aka kaddamar a birnin Niamey, da niyyar kawar da fasakwaurin kananan makamai da miyagun kwayoyi da ma uwa uba matsalar ta'addanci da ke addabar kasar da sauran makwabtanta. Tsarin na Flintlock da kasar Amirka ke jagoranta, a wannan karon ya shafi kasashen Nijar da Burkina Faso da kan iyakokinsu ke fuskantar matsanancin matsaloli na tsaro musamman ma na 'yan ta'adda da ke yakin sunkuru. Kama daga birnin Ouagadougou na Burkina Faso zuwa Niamey da Oualam da ma yankin Tahoua da ke makwabataka da Mali na daga cikin yankunan da askarawan kasashen duniya 26 da ke halarta gagarumin atisayen za su yada zango tare da kawo nasu tallafi ga al'umma, baya ga magance matsalolin tsaro da ke ciwa jama'ar yankunan tuwo a kwarya, kana sojojin da ke halartar gagarumin atisayin daga Afirka musamman ma na Nijar za su ci moriyar horo da sanin makamar aiki ta fannin soja daga takwarorinsu na Amirka

Donald Trump Republican Society Patriot Dinner South Carolina USA
Kasar Amirka ce ke jagorantan tsarin na FlintlockHoto: Getty Images/R.Ellis

Tasirin atisayen ga fannin tsaro

To ko wane tasiri wannan tsarin na Flintlock zai yi ga inganta tsaro a Jamhuriyar ta Nijar? Malam Kalla Moutary ministan tsaron Nijar da ya jagoranci kaddamar da gagarumiin atisayen ya ce:

"Tabbas daga bakin lokacin da soji suka ratsa kasa to duk wani mugun da ke nan zai ji tsoro, kuma duk da ya ke atisaye ne to amma duk inda soja dubu daya da 500 suka bi duk, wani mugu zai ja da baya. Ba shakka akwai wani abun da ke iya biyo baya da zai bamu damar tono duk wani mugun da ke cikin wannan yankin, muna son sanar da jama'a da cewa daga cikin kasashenmu ba bu wata ranar da mutum farar hula ko soja baya mutuwa a sanadiyar matsalolin tsaro"

Sansanin rundunar ta atisayen zai kasance a yankin Agadez wanda a ka'idance can ne mahadar ayyukan gagarumin atisayen. An dai shirya kawo karshen aikin sharar dajin a ranar 20 ga wannan wata na Afrilu da muke ciki, tare da bitar mahimman nasarorin da shirin askarawan fiye da dubu daya da 500 ya cimma a tsawon makwanni biyu.