1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Amnesty ta soki tsare 'yan fararan hulla

Salissou Boukari
May 26, 2018

Manyan kungiyoyin kasa da kasa guda 10 cikinsu har da Amnesty International da kungiyar Oxfam sun fitar da sanarwa kan halin da ake ciki na tsare jagororin kungiyoyin fararan hulla 26 a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/2yLqK
Logo von Amnesty International

Akasari ana tsare da jagororin kungiyoyin fararan hullar na Nijar ne tun a watan Maris da ya gabata bayan wata zanga-zanga da hukumomin kasar suka haramta wadda kuma ta haifar da dauki ba dadi tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro.

Kungiyar ta Amnesty International da ta Oxfam gami da sauran gamayyar manyan kungiyoyi takwas masu zaman kansu na kasa da kasa, sun yi kira ga gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar da ta sassauta lamarin ta hanyar sakin dukannin mambobin kungiyoyin fararan hulla da take tsare da su, tare da kawo karshen matsin lambar da ake yi wa sauran abokansu a cewar sanarwar.

Wannan mawuyacin halin da kungiyoyin fararan hullan na Jamhuriyar Nijar suka shiga ya dauki hankalin manyan kungiyoyin na kasa da kasa masu rajin kare hakin jama'a da ma kungiyoyi na ci-gaba a cewar Adama Coulibaly Darektan kungiyar Oxfam na yankin yammcin Afirka.