1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: A ceto mata da Boko Haram ta sace

Abdoulaye Mamane Amadou
August 3, 2017

A Jamhuriyar Nijar bangarori daban daban na martani kan umarnin shugaban kasar ga jami'an tsaro da su kubutar da mata da yara da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da a farkon watan jiya a garin Ngalewa na yankin Diffa.

https://p.dw.com/p/2he6E
Niger Flüchtlinge aus Nigeria
Hoto: DW/A. Cascais

Yanzu hakan dai ana ci gaba da samun mabanbantan ra'ayoyi game da umarnin na shugaba Issoufou, inda wasu ke ganin kalaman nas shi sun makara, a yayin da wasu kuwa ke ganin ya yi dai dai domin ya nuna gwamnati ta fara damuwa da wadanda a ka sacen ne. Shugaban kasa Mouhammadou Issoufou dai ya tabo batutuwa da dama da suka fi daukar hankali ciki har da batun tsarin iyali da gurbatar yanayi da kuma matsalar tsaro.

Ya kuma yaba wa daukacin jami'an tsaron kasar da ke fagen fama, dangance da kokarin da suke yi da ya ce ya  nuna kishin kasa da kare al'umma duk  kuwa da hare-haren ta'addanci da suke fuskanta lokaci zuwa lokaci. Wannan dai shi ne karon farko da wani babban jami'in gwamnati musamman ma shugaban kasa ke batun matan da aka sace tun a ranar biyu ga watan jiya wato Yuli, kana a cewar kungiyoyin da suke gwagwarmayar kubutar da matan babban abin alfahari ne jin wannan umurnin na shugaban kasa. Sai dai wasu masu gwagwarmaya kamar su Alhaji Salissou Amadou na kungiyoyin Sauvon le Niger na cewa duk da yake kalamun na shugaban kasa suna ratsa jiki, babu shakka akwai wani dan sakaci da gwamnatin ta yi musaman ma da ta dauki dogon lokaci kafin ta ce uffan kan wannan batun mai matukar mahimmanci. Shugaban a jawabin nasa, ya jaddada kalamai kan matakan da gwamnatin na renaisance ke dauka don kyautata rayuwar jama'a da tabbatar da tsaro da kuma bunkasar tattalin arziki duk da yake fannin na fuskantar tangal tangal.

Soldaten aus Niger bekämpfen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo