1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nigeria:Fina-finan Hausa na kaucewa a'aldu

April 10, 2018

Tsokacin 'yan wasan kwaikwayo a Najeriya a game da yadda suke kaucewa tsarin al'adu na rayuwar al'umma.

https://p.dw.com/p/2vmuQ
dw_Nollywood2
Hoto: DW/K.Gänsler

Tsoffin masu wasan kwaikwayo na arewacin Najeriya na nuna damuwarsu kan yadda matasan da ke wasan Hausa a yanzu, ke kwadayin tara dukiya a maimakon sanya aniyar kyautata tarbiyya tare da hadin kan al'umar Najeriyar. An dai jima da kokawa kan musamman yadda wasu fina-finan yanzun, ke kaucewa tsarin rayuwar al'ummar kasar, suna shiga na wasu nahiyoyin. Sai dai watakila ana ganin game da irin yadda jama'a ke ci gaba da yin tsokaci za a iya samun sauyi.