Nigeria tayi watsi da rahoton Human Right Watch | Labarai | DW | 12.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nigeria tayi watsi da rahoton Human Right Watch

Gwamnatin Nigeria ta soki lamirin Rahoton nan na Hukumar kare hakkin bil adama na human Right Watch, daya zargi yan siyasar klasar da take hakkoki na bil adama. A cewar gwamnatin kasar ta Nigeria, babu adalci a cikin rahoton na Human right Watch, daya shafi batu na take hakkin bil adama cin hanci da rashawa da kuma rikice rikice. Rahoton dai na Human Right Watch ya zargi yan siyasa ne dangane da yadda suke amfani da madafun iko wajen ingiza wutar rikice rikice da kuma daure gindin cin hanci da karbar rashawa. Bugu da kari rahoton ya kuma bukaci gwamnatin Umaru Yar´adua, kara daukar matakai na kashe kudaden gwamnati ta hanyar data dace.