1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nigeria tayi kasafin naira trillion 2.3 a shekarata 2007

Zainab A MohammadOctober 11, 2006
https://p.dw.com/p/Bu59

Shugaba Olusegun Obasanjo na Nigeria ya koka dangane da cigaban sace sacen maaikatan kamfanonin mai a yankin Niger Delta mai albarkatun mai a kudancin kasar.Sugaban Nigerian yayi wannan koke ne ayayinda yake gabatar da kasafin kudin shekarata 2007 a gaban majalisar dokokin kasar ayau.Yace a watannin uku na biyu acikin wannan shekarar ,Nigeria tayi asarar gangan danyan mai kimanin dubu 600,saboda wadannan rigingimu na yankin Deltan,kuma bisa dukkan alamu zaa cigaba da fuskantar wadannan matsaloli har zuwa karshen wannan shekara da muke ciki.Obasanjo yace sakamakon wadannan matsaloli da ake cigaba da fuskanta,kudaden mai da za a samu a wannan shekara zasu tasamma dala billion 4.3,wanda ya gaza abunda aka tsara tun da farko.

A kame kame na baya bayan nan dai,a jiya talata ne matasa a jihar Bayaelsa dakle yankin na Niger Delta ,suka kai somame cibiyar kamfanin mai na Shell,inda sukayi awon gaba da maaikata 46.Tun daga watan Augustan daya gabata dai,sace sacen maaikatan mai ya dada yin tsamari,abangaren matasa masu neman hakkin su daga albarkatun mai da yankin ke samarwa.