Nigeria ta nemi diyyar dubban miliyoyin daga kamfanin Pfizer
June 5, 2007Talla
Nigeriya ta nemi diyyar dala miliyan dubu 7 daga kamfanin harhada magunguna na Amirka wato Pfizer bisa yin gwajin wasu magunguna ba da izini ba. Gwajin sabbin magungunan da aka yi a jihar Kano daga shekara ta 1996 zuwa ta 2000 yayi sanadiyar mutuwa ko kuma yiwa kananan yara kimanin 200 illa. To sai dai kamfanin yayi watsi da wannan zargi.