Nigeria na binciken rashawa da ya hadar da Siemens | Labarai | DW | 19.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nigeria na binciken rashawa da ya hadar da Siemens

Shugaba Umaru Musa ‚yar Adua na tarayyare Nigeria,ya bada umurnin gudanar da bincike dangane da zargin rashawa da cin hanci daya kunshi kamfanin sadarwanan na Jamus na Siemens,da wasu tsofaffin ministocin kasar ,domin samun kwangila.Kakakin shugaban kasar Olusegun Adeniyi,yace an umurci dukkan hukumomin tsaro da abun ya shafa ,dasu gudanar da dukan bincike dangane da wannan zargi,domin daukar matakan hukunci kann wanda aka samu da laifi.