Niger za ta kori baƙi larabawa daga kasar ta | Labarai | DW | 25.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Niger za ta kori baƙi larabawa daga kasar ta

Gwamnatin Niger ta sanar da aniyar ta ta korar larabawa baki yan asalin Chadi su kimanin 100,000 zuwa kasar su ta asali. Gwamnatin ta baiyana daukar wannan matakin ne da nufin magance matsalolin fadce fadace a tsakanin wannan kabila da sauran alúmomin jihar Diffa dake iyaka da kasar Tchadi. Ministan alámuran cikin gida na kasar Niger Munkail Mudi yace zaá gudanar da korar bakin ne cikin nutsuwa da kwanciyar hankali bisa rakiyar jamián soji izuwa kan iyaka. Wasu daga cikin bakin larabawan sun shafe tsawon shekaru a kasar ta Niger. Shugaban kasar ta Niger Tanja Mammadu ya bada kulawa ta musamman wajen tabbatar da tsaro da kariya a wannan yankin.