1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Niger yuwan a cikin makarantu boko

April 2, 2010

Matsalar ƙaranci abinci a Niger na sa yan maranta boko zuwa ci rani

https://p.dw.com/p/MmN1
Wasu yara na garin Karey Gorou)Hoto: AP

An bada rahoton cewa yan makaranta a jamhuriyar Niger na ƙauracewa makarantu boko cikin ƙayuka zuwa ci rani a cikin mayan brine dake makobtaka da ƙasar saboda matsalar ƙarancin abincin da ake fama da shi.Sanarwa wanda gwamnatin ƙasar ita da kan ta ne ta bayyana a karshen wani taron majalisar ministoci,ta ce a cikin yankunan damagaram dake a tsakiyar kudancin kasar na ne aka fi samu yawan yan makarantar da suka daina yin karatun boko musamunma a garin Taketa.Yankin dai na Zinder na ne inda matslar ta rashin abinci ta fi yi ƙamari, kuma wata ƙungiyar mai zaman kan ta ta Oxfam ta ce a cikin watanin na gaba masu zuwa yawan adadin mutane dake fama da yunwar zai iya ƙaruwa zuwa milliyon goma.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita : Abdullahi Tanko Bala