Niger Delta: An nemi dakatar da kai hari a yankin mai arzikin man fetir | Labarai | DW | 21.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Niger Delta: An nemi dakatar da kai hari a yankin mai arzikin man fetir

Tsofaffin 'yan bindigar yankin Niger Delta a Najeriya sun bukaci 'yan yankin da suke kai hare-hare wajen tonon mai da iskar gas da su gaggauta dakatar da yin hakan.

'Yan bindigar na tsohuwar kungiyar nan ta MEND suka ce wannan hare-haren ba su da wani alfanu kuma yin hakan yunkuri ne na kawar da hankalin gwamnatin kasar daga yin aikin da ya kamata ta yi wa al'umma.

A wata sanarwa da tsofaffin 'yan tawayen suka fidda, sun ce ya kamata a dafa wa Shugaba Muhammadu Buhari don samun sukunin cika alkawuran da ya dauka kan yankin na Niger Delta. A ranar Juma'a dai gwamnatin ta Najeriya ta umarci jami'an tsaron kasar da tsaurara matakan tsaro kan wuraren da ake tonon mai a yankin bayan da 'yan bidiga suka dawo da kai hare-hare.