Niersbach ya yi murabus | Labarai | DW | 09.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Niersbach ya yi murabus

Wolfgang Niersbach ya kasance shugaban kungiyar kwallon kafar Jamus tun daga shekara ta 2012, kuma ya ce ya yi murabus bisa zargin cin hanci amma ya san bai aikata wani laifi ba.

Shugaban kungiyar kwallon kafan Jamus Wolfgang Niersbach ya yi murabus sakamakon wani zargin da ake yi da ya danganci biyan kudi ga hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, inda ya ke ba da hujjar cewa ya dauki alhaki a siyasance duk da cewa bai yi wani abin da ya sabawa doka ba.

Wannan kudi wanda ya danganci kofin kwallon kafa na duniya na shekara ta 2006 da aka yi a Jamus, ya ma kai ga gudanar da bincike kan shugaban kungiyar kwallon kafan mai murabus dangane da kin biyan kudaden haraji, har ma da wasu karin jami'an kungiyar biyu.

Niersbach wanda ya kasasnce shugaban kungiyar kwallon kafan na Jamus tun shekara ta 2012 mamba ne na kwamitin zartarwar FIFA da kungiyar kwallon kafar Turai, UEFA kuma da an yi zaton zai maye gurbin Michel Platini shugaban UEFA