1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netanyahu ya lashe zaben shugaban jam´iyar Likud ta ´yan ra´ayin mazan jiya

December 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvFg

Tsohon FM Isra´ila kuma rikakken dan ra´ayin rikau Benjamin Netanyahu ya lashe zaben shugaban jam´iyar Likud dake jan ragamar mulki a Isra´ila. Yanzu haka dai shi zai gaji FM Ariel Sharon wanda ya fice daga jam´iyar ta Likud kuma ya kafa sabuwar jam´iya da ake kira Kadima cikin watan jiya. Netanyahu dai ya yi ta kamfen din nuna adawa da janyewar Isra´ila daga Zirin Gaza a cikin watan agusta, inda ya zargi Sharon da mika kai ga bukatun sojojin sa kai na Falasdinawa. A kuma halin da ake ciki a yau za´a sallami FM Sharon daga asibiti bayan an yi masa jiyar wata kwarya-kwaryar mutuwar jiki. Likitoci sun ce FM na cikin koshin lafiya. A gobe laraba majalisar dokokin Isra´ila zata yi zaman ta na karshe gabanin zaben da za´a gudanar cikin watan maris mai zuwa.