Netanyahu ya gana da Obama a Fadar White House | Labarai | DW | 24.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Netanyahu ya gana da Obama a Fadar White House

Firaministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya gana tare da shugaba Barack Obama na Amurka a fadar White House

default

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu a fadar White House

Firaministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya gana tare da shugaba Barack Obama na Amurka a fadar White House. Ganawar ta zo ne bayan jawabin da Netanyahu yayi a gaban majalisar dokokin Amurka, inda yake bayyana fargaban jinkirta tattaunawar zaman lafiyar yankin Gabas Ta Tsakiya har nan da shekara guda, muddin Palasɗinawa basu dakatar da buƙatar su ta neman daina gine-ginen matsugunan Yahudawa ba. Gine-ginen da ministan harkokin wajen Jamus Giudo Westerwelle yace Jamus da Turai suka yi imanin shike hana ruwa gudu a shirin zaman lafiyar yankin Gabas Ta Tsakiya. An dai yi ganawar ta Obama da Netanyahu ne a bayan fage.

A waje ɗaya kuma sakataren harkokin wajen Birtaniya David Milliband ya sanar da korar wani jami'in ofishin jakadancin Israila dake London. Birtaniya ta ɗauki wannan mataki ne domin nuna fushin ta da hannun da Israilan keda shi wajen samar da wasu jabun fasfuna ga 'yan ƙasar ta Israila da ake zargi da kisan wani kwamandan dakarun Hamas a birnin Dubai a watan Janairun bana. A jawabin da ya gabatar a gaban majalisar dokokin Birtaniya, Milliband yace matakin na Israila cin amanar dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu ne. Milliband yayi fatan nan gaba Isra'ilan ba za ta sake gangancin anfani Fasfunan Birtaniya wajen aika-aika irin wannan ba. Tuni dai Isra'ila tace ba za ta maida martani game da matakin ba.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Mohammad Nassir Awal