Neman tsige Zuma daga madafun iko | Labarai | DW | 05.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman tsige Zuma daga madafun iko

Majalisar dokokin Afirka ta Kudu tana yunkurin tsige Shugaba Jacob Zuma da mulki bisa larfin karya dokoki.

A wannan Talata majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu tana yunkurin tsige Shugaba Jacob Zuma, bayan kotun tsarin mulki ta same shi da taka dokokin kasa, kan kudaden da aka kashe na kyara masa gidansa.

Akwai yiwuwar Shugaba Zuma zai kai labari saboda ana bukatar kashi biyu bisa uku na kuri'un 'yan majalisa kafin tsige shugaban, wanda yake da goyon bayan jam'iyyar ANC mai mulki wadda take da akasarin mambobin majalisar.

Ita dai jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu ta gudanar da taruka tun bayan hukuncin kotun da aka samu Shugaba Jacob Zuma da karya dokokin kasa, amma jam'iyyar ta yi watsi da shirin tsige shugaban.