Neman taimakon Amirka domin warware rikicin Somalia | Labarai | DW | 12.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman taimakon Amirka domin warware rikicin Somalia

Kenya ta zargi Amirka da rashin taka rawar da ta dace wajen kawo karshen rikicin Somalia

default

Shugaba Kibaki na Kenya da Abdullahi Yusuf na Somalia

Gwamnatin kasar Kenya ta bayyana damuwar ta game da tattaunawar da ake yi tare da hukumar bunkasa kasashe ta Amirka domin tallafawa Somalia. A cikin wata hirar da aka yi da shi - jiya Litinin a birnin Washington na Amirka, mukaddashin Firaministan Kenya Uhuru Kenyata, wanda ya bayyana wanan damuwar, ya kuma ce, yana bukatar kara samun hadin kan kasar Amirka wajen daidaita lamura a kasar ta Somalia, da kuma yaki da masu fashin jiragen ruwa a yankin gabashin Afirka ma baki daya.

Kenyata ya ce a baya jami'an Amirka ciki harda mataimakin shugaban kasar Joe Biden, sun baiwa kasar sa tabbacin samun agaji bayan ta samar da sauye sauye ga tsarin mulkin kasar. Sai dai ya ce abin mamaki gashi bayan shugaban kasar ya sanya hannu akan sabon tsarin mulkin, har yanzu hukumomin bayar da agaji a Amirka suna nanata cewar, sai sunga hujjojin da ke tabbatar da cewar, kasar Kenya ta sami ci gaba wajen yaki da cin hanci. Ya ce in har da gaske suke yi, to me yasa suke ta canza manufofin su?

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu