1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman mafita ga batun 'yan gudun hijira

Pinado Abdu WabaSeptember 3, 2015

Kasashen Italiya da Faransa da Jamus na neman sauya dokokin da za su saukake wa 'yan gudun hijira hanyoyin samun mafaka a Turai.

https://p.dw.com/p/1GQfL
Flüchtlinge Bahnhof Budapest
Hoto: DW/L. Scholtyssyk

Firaministan Italiya Matteo Renzi ya ce bai kamata Turai ta tsaya kadai a kan hotunan masu gudun hijirar da kafafen yada labarai ke wallafawa ba, amma wajibi ne su dauki kwararan matakai ta yadda za'a gani a kasa. Firaministan ya fadi haka ne wuni daya bayan da aka wallafa hoton wani karamin yaro da ruwa ya wanko shi yana kwance da fuskar sa a kasa, kusa da garin Bodrum, daya daga cikin manyan wuraren shakatawar Turkiyya, kafin wani dan sanda ya kawar da shi.

Renzi ya ce wannan matsala ta kowa ce, kuma akwai bukatar mutane su yi la'akari da cewa irin tallafin da za a iya kaiwa yanzu, yana bukatar nazari da hangen nesa.

Italiya ta bi sahun kasashen Jamus da Faransa, wadanda ke kira da a sauya wasu daga cikin dokokin Turai domin a mutunta 'yancin bayar da mafaka ga wadanda ke bukata, gabannin taron da ministocin harkokin wajen Turan za su gudanar a karshen wannan makon.