1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman kuri'u da ayyukan kasa a Nijar

Abdoullaye Mammane Amadou daga NiameyJanuary 15, 2015

Yayin da shugaban kasar ke kaddamar ayyukan gina hanyoyi a birnin Niamey, wasu 'yan adawar kasar sun fito suna masu zargin cewar shugaban ya fara yakin zabe ne.

https://p.dw.com/p/1ELID
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Mahamadou Issoufou: shugaban kasar NijarHoto: DW/M. Kanta

A wani abu da ke nuna dangantaka na kara tsami tsakanin 'yan hamayyar kasar da shugaban kasar Nijar mai ci yanzu Alhaji Mouhamadou Issoufou, masu adawa na kallon shugaban da amfani da ayyukan raya kasa wajen kamfe. Tuni dai 'yan adawar suka sha alwashin kayar da shi a zabe 2016 mai zuwa.

Shugaban kasar Nijar Mouhamadou Issoufou ya bayyana muhimman ayyukan da ya yi wa kasar Nijar shekaru 4 bayan rantsar da shi a karagar mulki, to amma sai dai kalaman na zuwa ne a yayin da 'yan adawar kasar ke zargin shugaban da wasu manufofin farfagandar zabe ta hanyar amfani da ayyukansa domin makalewa a kan madafun ikon kasar, dalilan da suka sa kenan ma suka farga tare da kauracewa duk wata gayyatar da shugaban zai yi musu domin kaddamar da wasu ayyukan da zai yi wa 'yan Nijar din da 'yan adawar ke cewar su suke da magoya baya mafi rinjaye.


A cewar Ali Sabo mataimakin shugaban Jam'iyyar MNSD Nasara mai adawa ba tun yau ba shugaban kasa yake tafe da wadannan manufofin:

"Shugaban kasa tun da ya kama iko ya so ya saka gundumomi a cikin tsarinsa na gaggawa domin ya kada muna girma, kada mu samu 'yan majalisu da yawa, baya ga wannan an yi kidayar jama'a kaga yadda a ka yi jihar Tahoua tafi yawan mutane wato jiharsa ta haihuwa, Maradi aka rage mata, Tillaberi, suma Zinder haka duk wadannan abubuwan yana yi ne domin yana hangen zabe na 2016".

Alhaji Saini Oumarou Oppositionspartei MNSD Nasara im Niger
Alhaji Saini Oumarou na MNSD Nasara mai adawa a Nijar.Hoto: DW/M. Kanta


To amma sai dai tuni mataimakin daraktan fadar shugaban kasar ta Nijar Alhaji Ibrahim Yacouba ya mayar da martini kan kalaman da 'yan adawar ke yi:

"Duka tubalin da aka aza kana iya bincike ka gani, wane tubali aka aza wanda ba'a cika ba, idan an aza tubali ba'a cika ba to kana iya cewar anyi shi ne saboda yakin zabe, abinda aka dauka na alkawura don ci gaban kasa nan da wata goma sha biyu sai ka dawo ka gani abinda akayi da wanda ba'ayi ba".