Neman agaji ga ƙasar Benin | Labarai | DW | 03.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman agaji ga ƙasar Benin

An buƙaci ƙasashen duniya su bada agaji don tallafawa Jamhuriyar Benin, wanda ambaliyar ruwa ta yi wa ɓarna

default

Shugaban Jamhuriyar Benin, Thomas Boni Yayi.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙira ga ƙasashen duniya da su kawo ma jamhuriyar Benin ɗauki, biyo bayan ambaliyar ruwa da ta shafi dubban mutane. Majalisat tace ta na buƙatar agaji na kimanin dala miliyan 47, don kai ɗauki a jamhuriyar ta Benin. Wata sanarwar da MDD ta fitar, tace mutane fiye da dubu 100 suka rasa gidajensu, kana masifar ta shafi a ƙalla mutane dubu 680,000. Inda kuma aka yi asaran dabbobi da amfanin gonaki da sauransu. Yanzu kuma ana saran alƙaluman za su ƙaru, a daidai lokacin da ake hasashen samun ƙarin wani ruwan sama mai ƙarfi, cikin kwanaki dake tafe. MDD tace ta na buƙatar kuɗinne domin sayan abinci da magunguna ga dubban mutannen da ambaliyar ta shafa. Dama dai a ƙasar ta Benin cutar kwalara ta yi ɓarna mai yawa, inda aka ƙiyasta mutane 800 suka mutu sakamakon cutar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal