Nelson Mandela ya cika shekaru 92 da haifuwa | Labarai | DW | 13.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nelson Mandela ya cika shekaru 92 da haifuwa

A ranar lahadi mai zuwa Tsofon Shugaban ƙasar Afrika ta Ƙudu Nelson Mandela ke cika shekaru 92 a duniya.Majalisar Dinkin Duniya ta yi ikirarin ranar ta 18 ga watan Yuli ranar Mandela

default

Nelson Mandela

Shugaban Afrika ta ƙudu na farko baƙar fata Nelson Mandela zai cika shekaru 92 a duniya a ranar lahadi mai zuwa indan Allah ya kaimu.Wani jikansa dake magana da manema labarai ya shaida cewa za a gudanar da bukukuwa a gidansa dake a birnin Johannesburg, tare da halartar shugaban ƙasar mai ci yanzu Jacob Zuma da zai yi jawabi.A shekarun baya dai Mista Mandela na gudanar da irin wannan bukukuwan ne tare da Jama'ar ƙawyen Qunu inda ya girma.

Wannan bikin kuma da za a yi shi ne a dadai  da ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi iƙirarin ranar Mandela ta 18 ga watan yuli,  wacce nan gaba a kowace shekara za a riƙa karramawa domin kyatatuwar samun zaman lafiya a duniya.

Mawallafi: Abdopurahamane Hassane.

Edita       : Ahmad Tijani  Lawal.