Nawaz Sharif ya sauka a brinin Jeddah bayan an koreshi daga Pakistan | Labarai | DW | 10.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nawaz Sharif ya sauka a brinin Jeddah bayan an koreshi daga Pakistan

Tsohon FM Pakistan Nawaz Sharif ya isa a birnin Jiddah na kasar Saudiya sa´o´i kalilan bayan an sake korarsa daga kasarsa. Wani dan diplomasiyar Saudiyya ya ce jami´an kasar suka tarbi Sharif a dakin saukar manyan baki na filin jirgin saman birnin na Jiddah. Da sanyin safiyar yau litinin dai jim kadan bayan saukar sa a Islamabad bayan ya shafe shekaru 7 yana gudun hijira a ketare, hukumomin Pakistan suka kori tsohon FM Pakistan Nawaz Sharif zuwa kasar Saudiyya. A lokacin da ya isa filin jirgin saman na Islamabad Sharif mai shekaru 57 ya fadawa manema labarai tun a cikin jirgi cewa bai san abin da zai faru a kan shi ba.

Sharif:

Ya ce “Ban san abin da ke faruwa ba hakan bai taba faruwa ba, suna son su dagula hali da ake ciki. Wata majiya ta nuna cewa zasu kwashe mu zuwa wani wuri maimakon su ba mu izinin shiga kasar.”

Tun a cikin shekarar 1999 Musharraf wanda a wancan lokaci shi ne hafsan sojin Pakistan ya hambarad da FM Sharif a wani juyin mulkin soji.