Nawaz Sharif ya dage kan komawa Pakistan duk da gargaɗin da ake masa | Labarai | DW | 08.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nawaz Sharif ya dage kan komawa Pakistan duk da gargaɗin da ake masa

Tsohon FM Pakistan Nawaz Sharif ya dage cewa zai koma Pakistan don kalubalantar shugaba Pervez Musharraf duk da katsin lamba da yake sha daga Saudiya na ya girmama wata yarjejeniya ta ci-gaba da zaman gudun hijira a ketare. A ranar litinin Nawaz Sharif wanda sau biyu yana darewa kan kujerar FM, zai tashi daga London zuwa Islamabad duk da barazanar kama shi da jami´ai suka yi. a cikin shekarar 1999 Musharraf ya hambarad da gwamnatin Sharif a wani juyin mulkin soji. An yanke masa hukunci daurin rai da rai gabanin a sake shi zuwa hijira a Saudiya. Bayan wata ganawa da shugaba Musharraf da dan majalisar kasar Lebanon Saad Hariri a yau asabar shugaban hukumar leken asirin Saudiyya Muqrin bin Abdulaziz Al Saud ya ce ya kamata tsohon FM ya girmama yarjejeniyar da ya kulla da hukumomin Saudiyya na kada ya shiga Pakistan har tsawon shekaru 10.