Nawaz Sharif ya cike takardar tsayawa takara | Labarai | DW | 26.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nawaz Sharif ya cike takardar tsayawa takara

Tsohon firaministan Pakistan Nawaz Sharif ya cike takardunsa na tsayawa takara a babban zaɓe da zaa gudanar a watan Janairu,kwana guda bayan dawowar sa daga gudun hijira a Saudiya.Sai dai kuma rahotanni sun ce Antoni Janar na Pakistan ya fadi cewa akwai yiwuwar dakatar da Sharif daga tsayawa a babban zaben tunda tuni aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai kafin ya tafi gudun hijirar.Watanni biyu da suka shige ne dai yunƙurin Nawaz Sharif na kawo ƙarshen gudun hijirar ya ci tura a lokacin da shugaba Parvez Musharraf ya bada umurunin sake maida shi Saudiya bayan ya koma gida.