1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Na'urar sarrafa madara a Najeriya

Wani matashi ya kirkiro wata na'urar wadda cikin sauki take sarrafa madara domin bunkasa yaynayin samar da madara tsakanin mutane a Najeriya.

Wani matashi mai suna Colenious Philip dake zaune a cikin jihar Kano arewa maso yammacin Najeriya ya sami nasarar kirkiro da naurar sarrafa duk wata madara domin yin yougurt wacce kuma aka fara amfani da ita a yayin da a hannu daya matasa ke samun hanyar da zasu dogara ita don samun abababen more rayuwa.

Matashin Colenoius Philip dan shekaru 25 a duniya wanda yake dan asalin jihar Kaduna ne dake zaune a jihar Kano arewacin Najeriya shima za a iya cewar ya kama hanyar matasan dake sahun gaba wajen kokarin kawo wani sauyi a tsakanin al'umma, a inda a sakamakon aiki tukuru ya samar da naurar sarrafa madara daya kira da suna yougurt mixer ya bayyana makasudin daya sanya shi samar da naurar.

Kazalika matshin yayi nuni da cewar na'urar sarrafa madarar tana amfani da hasken wutar lantarki kana kuma mutane masu yawa na amfani da ita.

Yanzu haka dai matashin mai suna Philip Colenoius na kokarin samar da naura madarar mai amfani da sola maimakon amfani da hasken wutar lantarki domin amfanin jama'a.