NATO za ta kara yawan dakarunta a kasashen gabashin Turai
October 8, 2015Kasashen Jamus da Amirka na son a girke karin dakarun kungiyar kawancen tsaro ta NATO cikin kasashe membobinta da ke gabashin Turai. Rahotanni sun ce ana iya tura daruruwan sojoji da za su ba da horo a kasashen Poland da Latviya da Estoniya da kuma Litawun wadanda ke fuskantar barazana daga Rasha dangane da rikicin kasar Ukraine.
A dangane da rikicin kasar Siriya kuwa inda yanzu haka Rasha take luguden wuta a kan mayakan IS, kungiyar ta NATO ta ce tana kuma tunanin karfafa yawan sojojinta a kasashe irinsu Turkiya. Babban sakataren kungiyar Jens Stoltenberg ya fadi hakan lokacin bude taron ministocin tsaro na kawance a birnin Brussels, inda ma ya kara da cewa.
"Muna fuskantar kalubale daga bangarori daban-daban. Ga rikice-rikice da rashin tsaro da kuma matsalar 'yan gudun hijira sakamakon rikicin a kasashen kudancinmu. NATO tana daukar matakan bai-daya na karfafa tsaronta mafi girma tun kawo karshen yakin cacar baka."