NATO tayi marab da neman taimako da AU tayi a gereta | Labarai | DW | 08.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO tayi marab da neman taimako da AU tayi a gereta

Sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Hoop Scheffer yayi maraba da bukatar da kungiyar taraiyar Afrika ta mika na neman karin taimako ga dakarunta da suke yankin Darfur na kasar Sudan.

Dakarun kungiyar ta AU da yawansu ya kai 7,000 suna cikin matukar matsalar rashin kudi da kayan aikin wanzar da zaman lafiya a yankin da tashe tashen hankula suka tilasatawa fiye da mutane miliyan 2 da rabi suka tsere daga gidajensu.

Ita dai kungiyar tsaro ta NATO tana bada taimako kwasar dakarun AU tare da basu horo,kuma tayi alkawarin ci gaba da bada wannan taimako muddin dai AU ta mika bukatar yin hakan.

Sakataren na NATO yace ya samu wasika daga shugaban AU Alpha Umar Konare cikin wannan mako wadda ta bukaci taimakon NATO tare da fadada aiyukanta ayankin,wadda yace tuni ya mika gaban taron ministocin tsaron kungiyar.

Kodayake Konare ya jaddada cewa,basu bukatar kasancewar sojin kasashen yamma a yankin,ana kuma sa ran mika aiyukan AU ga MDD a karshen shekara idan Sudan ta bada amincewarta.