NATO ta yi gargaɗin taɓarɓarewar al’amura a Afghanistan. | Labarai | DW | 09.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO ta yi gargaɗin taɓarɓarewar al’amura a Afghanistan.

Babban kwamandan rundunar ƙungiyar ƙawance ta NATO a Afghanistan, Laftanan-Janar David Richards, ya yi gargaɗin cewa, idan ba a ɗau matakan inganta halin rayuwar jama’ar ƙasar ba, to za a sami haɓakar magoya bayan ƙungiyar Taliban. Ƙasar ta Afghanistan dai, inji kwamandan, na cikin wani hali ne na sauyi. Idan ko a cikin watanni 12 masu zuwa ba a sami wani ci gaba a yunƙurin inganta halin rayuwar jama’ar ƙasar ba, to da yawa daga cikinsu ne za su mai da alƙiblarsu wajen nuna cikakken goyon baya ga ƙungiyar Taliban.