1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NATO ta ƙaddamar da gagaramin hari a Tora Bora

Rundunar ƙasa da ƙasa a Afghanistan, ta bayyana ƙaddamar da wani gagaramin shiri, na fattatakar mayaƙan Taliban, a yankin Tora Bora, dake gabacin ƙasar, yankin da a ka ɗauka tamkar wata maɓuyar yan taliban.

Kakakin rundunar tsaro ta ISAF, kaptain Vanessa Bowman ya ce dakarun sun darkaka a wannan yanki, ta hanyoyin ƙasa da sama, da zumar zaƙulo mayaƙan Taliban.

A shekara ta 2001, wasu rahotani sun nunar da cewa shugaban ƙungiyar Alqa´ida Usama Bin Laden, na ɓoye a wannan tsauni na Tora Bora.

Cemma sijojin Amurika, tare da abokan ƙawancen su, sun sha ƙaddamar da irin wannan hari a duwatsun Tora Bora, ba tare da cimma nasara ba.

Harin ƙarshe ya wakana ranar 3 ga watan juli da ya wuce.