1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO sun kashe mutane 45 a Afganistan

June 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuIB

Haren haren jiragen saman yaki na kungiyar tsaro ta NATO a kasar Afganistan,ya kashe akalla mutane 45.Rahotannin kafofin yada labaru na nuni dacewa akwai fararen hula 25 daga cikin wadanda dakarun wsuka kashe,a harin da suka kai a daren jiya ,ayayinda ake zargin sauran da kasancewa mayakan kungiyar Taliban.Yansanda dake gunduwar Helmand ,inda nan ne aka kai hare haren na daren jiya,sun bayyana cewa cikin kuskure dakarun na NATO sun kai hari a gidajen jamaa.To sai nasu bangaren ,jamian tsaron sun sanar dacewa harin na mai kasancewa martani ne dangane da wasu hare hare da mayakan Taliban suka kai,inda bayan nan ne suka boye a gidajen mutanen da aka kaiwa harin.