1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

NATO na waiwaye kan cika shekaru 75 da kafuwa

April 4, 2024

Ministocin harkokin wajen kasashe mambobin NATO na gudanar da bikin cika shekaru 75 da kafa kungiyar, tare da jaddada bukatar tallafawa kasar Ukraine ta kowacce fuska domin tunkarar abokiyar gabarta kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/4ePUe
Tutocin kasashe mambobin kungiyar NATO a shedikwatar kungiyar da ke birnin Brussels na kasar Belgium
Tutocin kasashe mambobin kungiyar NATO a shedikwatar kungiyar da ke birnin Brussels na kasar BelgiumHoto: La Nacion/ZUMA Wire/Imago Images

A taron da ake gudanarwa a birnin Brussels na kasar Belgium, ministocin harkokin wajen zasuyi waiwaye kan daftarin da aka rattabawa hannu na kafa kungiyar NATO a birnin Washington na kasar Amurka, a ranar 4 ga watan Afrilun 1949.

Karin bayani: NATO za ta ci gaba da ba Ukraine makamai

Sakatare Janar na kungiyar Jens Stoltenberg, ya ce zasu ci gaba da aiki tare wajen karfafa alakar da ke tsakanin kasashe mambobin kungiyar kuma zasu ci gaba da aiki da kawayen kungiyar domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Karin bayani: Sweden ta zama memba na 32 na kungiyar NATO

Kungiyar ta fara da mambobi 12 har zuwa 32, kasashen da suka shiga kungiyar ta NATO a baya bayannan sun hadar Sweden da Finland da suka shiga kungiyar domin jaddada goyon baya ga Ukraine tun bayan farmakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine a 2022.